Jami’an Iran sun yaba da nasarorin da aka samu a yayin halartar  Pezeshkian a taron SCO

Jami’an Iran sun yaba matuka da irin nasarorin da aka samu a yayin halartar shugaban kasar Mas’ud Pezeshkian a taron kungiyar  Shanghai (SCO) a kasar

Jami’an Iran sun yaba matuka da irin nasarorin da aka samu a yayin halartar shugaban kasar Mas’ud Pezeshkian a taron kungiyar  Shanghai (SCO) a kasar China.

Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Kazem Gharibabadi ya bayyana cewa, Iran ta yi amfani da tsarin diflomasiyya a bangarori daban-daban a yayin taron kolin kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai (SCO) na shekara-shekara a kasar Sin.

Gharibabadi  ya bayyana hakan a wani sakon da ya wallafa a shafinsa na X, tsohon shafin Twitter a jiya Talata, inda ya yi bayani kan abubuwan da suka shafi taron, wanda shugaba Masoud Pezeshkian, wanda ke ziyarar aiki a kasar Sin ya aiwatar da su.

A cewar jami’in diflomasiyyar, halartar babban jami’in gudanarwa na kasar Iran a taron ya nuna yadda kasar take  aiwatar da irin wannan salon a sahihiyar diflomasiyya.

Ya kara da cewa, Pezeshkian ya gabatar da jawabai daban-daban guda biyu a taron SCO da SCO Plus, inda shugaban ya jaddada kyakkyawar rawar da Iran ke takawa wajen karfafa hadin gwiwar yankin ta hanyar gabatar da sabbin tsare-tsare.

SCO tana aiki a matsayin babbar ƙungiyar gwamnatocin yanki da ke mai da hankali kan haɗin gwiwar siyasa, tattalin arziki da tsaro.

Kasashen da suka kafa kungiyar a shekarar 2001 sun hada da China, Rasha, Kazakhstan, Kyrgyzstan, Tajikistan, da Uzbekistan. Iran ta shiga kungiyar ne a watan Yulin 2023.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted