Ministan harkokin wajen Iran ya jaddada aniyar Iran na bunkasa alaka da kasar Qatar a dukkan fannoni
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya yi nuni da kyakkyawar alakar da ke tsakanin Iran da Qatar, yana mai jaddada aniyar gwamnatin Jamhuriyar Musulunci ta Iran na bunkasa alaka da kasar Qatar a fannoni daban daban.
Wannan ya zo ne a yayin ganawar da ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya yi a birnin Doha a jiya Alhamis, tare da fira ministan Qatar kuma ministan harkokin wajen kasar Sheikh Mohammed bin Abdulrahman Al- Thani.
Taron ya tattauna batutuwa da dama da suka shafi bangarorin biyu, da suka hada da ci gaban huldar dake tsakanin kasashen biyu, da kuma ci gaban yankin, musamman a fagen Falasdinawa bayan yarjejeniyar tsagaita bude wuta, da kuma yanayin siyasar kasar Lebanon bayan zaben shugaban kasa da fira minista.
Tattaunawar ta ta’allaka ne kan keta yarjejeniyar tsagaita bude wuta da yahudawan sahayoniyya suka yi, da kuma abubuwan da suke faruwa a kasar Siriya, sun kuma tattauna tare da yin musayar ra’ayi kan yadda kasashen biyu ke ba da goyon baya ga ‘yancin kai, kwanciyar hankali da kuma ‘yancin yankin kasar Siriya.