Jakadan Syria A MDD Ya Yi Tir Da  Hare-haren Da “Isra’ila” Take Kai Wa Kasarsa

Wakilin kasar Syria din a MDD ya yi kira ga kwamitin tsaro na MDD da babban magatakardarta da su hana “Isra’ila” yin amfani da sauyin

Wakilin kasar Syria din a MDD ya yi kira ga kwamitin tsaro na MDD da babban magatakardarta da su hana “Isra’ila” yin amfani da sauyin mulki da aka samu a kasar tana kai hare-hare.

A wani taron manema labaru da ya yi a zauren MDD Qusay Dhahhak, wanda ya gabatar da taron manema labaru a jiya Litinin ya yi tsokaci akan hare-haren da “Isra’ila” take kai wa kasarsa inda ya ce, bisa umarnin da ya samu daga  sabuwar gwamnatin Syria, yana yin kira ga kwamitin tsaro da babban magatardar MDD da su hana Isra’ila cigaba da kai hare-haren da take yi.

Dhahhak ya cigaba da cewa,  wakilan Syria a MDD suna cigabada da gudanar da ayyukansu a matsayin wani sashe na daular Syria, kuma muna wakiltar al’ummar kasar Syria ne.

Har ila yau Dhahhak ya ce, muna cigaba da yin aiki tare da shugaban hukuma da kuma Fira minista, muna sauraron a kafa sabuwar gwamnati.

Kafafen watsa labarun Syria sun sanar da cewa; Ahmad Shar’a, wanda aka fi sani da Julani, da shi ne jagoran ‘yan tawaye da su ka kafa sabuwar gwamnati, ya  bai wa Muhammad al-Bashir umarnin kafa gwamnatin rikon kwarya a Syria.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments