Jakadan Iran A MDD Ya Jaddada Kawo Karshen Takunkumin Amurka Kan Kasar Cuba

Jakadan Iran a Majalisar Dinkin Duniya ya jaddada cewa: Dole ne a dage takunkumin da Amurka ta kakaba wa Cuba nan take Jakadan Iran kuma

Jakadan Iran a Majalisar Dinkin Duniya ya jaddada cewa: Dole ne a dage takunkumin da Amurka ta kakaba wa Cuba nan take

Jakadan Iran kuma Wakilin Dindindin a Majalisar Dinkin Duniya, Amir Sa’ed Irawani, ya jaddada cewa: Dole ne a dage takunkumin da aka sanya wa Cuba nan take ba tare da wani sharaɗi ba. Ya bayyana cewa: Kawo ƙarshen waɗannan matakan ba wai kawai zai samar da sauƙi ga al’ummar Cuba ba ne, har ma zai aika da saƙo mai haske da yanke hukunci ga duniya cewa zamanin tilastawa, mulkin mallaka, da rashin adalci na tattalin arziki ya ƙare.

Irawani ya jaddada a ranar Talata, a lokacin taron Majalisar Dinkin Duniya da aka keɓe don tattauna ɗage takunkumin Amurka kan Cuba, cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta ƙi amincewa da manufofin bangare guda na matakan tilastawa da Amurka ta daukan kan ƙasashe masu ‘yancin kai.

Jakadan Iran ya nuna cewa: Waɗannan manufofin bangare guda sun saɓa wa dokokin ƙasa da ƙasa, sun dogara ne akan girman kai da rashin haɗin kai, suna kawo cikas ga haɗin kan ƙasa da ƙasa, suna kawo cikas ga tsarin duniya, kuma suna lalata ruhin Yarjejeniyar Majalisar Dinkin Duniya. Ya jaddada cewa waɗannan matakan suna da mummunan tasiri ga ƙoƙarin inganta zaman lafiya, a yanki da kuma a duniya baki ɗaya, kuma suna zama babban cikas ga gina duniya mai karko da adalci, wanda yake da mahimmanci don cimma ci gaba mai ɗorewa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted