Jakadan Iran A Hukumar IAEA Ya Ce Takunkuman Kasashen Yamma A Kan Kasar Ba Za Su Yi Aiki Ba

Jakadan JMI a hukumar makamashin Nukliya Mohsen Naziri ya bayyana cewa sabbin takurawar da kasashen yamma, musamman Amurka suke wa kasarsa ba zasu yi tasiri

Jakadan JMI a hukumar makamashin Nukliya Mohsen Naziri ya bayyana cewa sabbin takurawar da kasashen yamma, musamman Amurka suke wa kasarsa ba zasu yi tasiri ba. Banda hakan zasu cutar da wadanda suka dora mana su,

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Naziri yana fadar haka a Jawabin da ya gabatar  a taron gwamnoni hukumar ta IAEA a birnin Geneva a jiya Laraba. Ya ce kasashen yamma ne suka jagoranci karin takunkuman tattalin arziki a kan Iran, ko kuma bayyana cewa Iran bata bada hadin kai da ta dace ga hukumar makamashin Nukliya ta duniya wato IAEA. Da kuma zargin kasar Iran da cewa tana kokarin mallakan makaman Nukliya.

Naziri ya zargin kasashne yamma kan rashin cika al-kawalin da suka dauka a yarjeniyar JCPOA na shekara ta 2015, inda Amurka ta fara da janyewa daga yerjeniyar da aka dauki shekaru biyu cur ana tattaunawa a kanta.

Yace Amurka ta fice daga yaerjeniyar a shekara ta 2018 da sunan shi ne yarjeniya mafi muni wanda Amurka ta taba sanyawa hannu, kuma zata tilastwa Iran amincewa da sabuwar yarjeniya da ita, ko kuma ta sha wahala, ko gwamnatin JMI ta rushe karkashin takurawar ta.

Banda haka kasashen Turai wadanda suke goyon bayan Amurka sun ki cika nasu alkawulan a cikin yarjeniyar ta JCPOA.

Naziri Asl ya bayyana cewa martanin da Iran ta mayar shi ne, rage abinda yah au kanta a yarjeniyar, , wanda ita kanta Yarjeniyar ta bada damar yin haka a duk lokacinda dayan bangaren ya saba alkawulan da ta dauka a cikinta.

Ka’ida ta 26 da 36 na yarjeniyar ta bawa Iran wannan damar, na sabawa yarjeniyar don dawo da dayan bangaren kan abinda yakamata ya yi.

Ya kuma kara da cewa kasashen yamma basu da damar sake maida takunkuman tattalin arziki kan Iran saboda sune suka sabawa yarjeniyar.

Daga karshe ya ce Iran zata koma kan amfani da yarjeniyar ne kawai idan kasashen yamma sun dauke mata dukkan takunkuma tattalin arzikin da suka dora mata.

Sannan yace kasashen Ingila Faransa da Jamus sun sabawa kudurin kwamitin tsaro na MDD mai lamba 2231 wanda yake goyon bayan JCPOA.

Daga karshe yayi kira da gwamnonin hukumar ta IAEA da su maida hankalinsu wajen dabbaka kudurin na 2231.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments