Jagoran Yan Gana Da Tawagar Shuwagabannin Kungiyar Hamas A Nan Tehran

Jagoran juyin juya halin musulunci a nan Iran ya gana ta tawagar shoura ta kungiyar Hamas a safiyar yau Asabar a nan Tehran inda ya

Jagoran juyin juya halin musulunci a nan Iran ya gana ta tawagar shoura ta kungiyar Hamas a safiyar yau Asabar a nan Tehran inda ya bayyana cewa mayakan kungiyar sun sami nasara a kan Amurka da HKI a yakin da suka dora masu na tsawon watanni 15.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Imam Sayyid Aliyul Khaminae yana cewa tsagaita wuta da aka samu bayan wannan lokaci mai tsawo na fafatawa yayi dai-dai.

Tawagar shuraa ta Hamas din dai sun hada da shugaban riko na kungiyar Khalil Al-Hayya, shugaban majalisar shoora ta kungiyar Muhammad Ismail Darwish da sauransu.

Jagoran ya kara da cewa nasarar da mutanen Gaza suka samu a kan Amurka da kawayenta misdaki nan a ayar Alkur’ani inda All..T yake cewa {Sau da dama kamar kungiya ta sami nasara a kan gayya babba, tare da izinin All..} Ya ce kun saminasara a kan HKI da Amurka tare da taimakon All..sannan All..ya hanasu cimma ko guda daga cikin manufofinsu na fara yakin.

Sayyid Khamanae ya cewa, mutanen Gaza sun sha wahala kimani shekara da rabi, amma karshen al-amari shine nasarar da kuka samu, kuma nasara ce na gaskiya kan karya. Jagoran ya yabawa masu tattaunawar Hamas wadanda suka sami nasarar kubutar da daruruwan falasdinawa daga gidajen Yarin yahudawan ba bisa sonsu ba.

Yace a tsagaita wuta na farko bayan kin na kwanaki 45 an yi musayar yahudawa 33 da Falasdinawa 2000 sannan musayar da ake yi bayan tsada yakin ma yana da kyau.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments