Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran ya ce: Dukkanin Jagororin shiriya na iyalan gidan Manzon Allah tsarkaka {a.s} sun kasance suna kokarin wanzar da shari’ar Musulunci ne a kan doron kasa
Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran Ayatullah Sayyid Ali Khamenei, yayin da ya karbi bakwancin mambobin kwamitin zaman taron karawa juna sani na cibiyar Imam Ridha (a.s) a yau Litinin, ya tabbatar da cewa: Dukkanin jagororin shiriya na iyalan gidan Manzon Allah tsarkaka {a.s} sun kasance suna gwagwarmayar wanzar da shari’ar Musulunci ne a kan doron kasa.
A cikin bayanin da ya gabatar a zaman taron, Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya yi nuni da cewa: Akwai kura-kurai da dama a fagen fahimtar manufofin jagororin shiriya, yana mai cewa: A wasu lokuta wasu sun fi mai da hankali ne sosai kan wani bangare na rayuwarsu, tare da yin watsi da sauran bangarorin, yayin da a wasu lokuta ba a mai da hankali ga abin da ke faruwa a fagen tushen rayuwarsu.