Iran : Dole A Tabbatar Da Tsaron Yankin, Ba Tare Da Taimakon Ketare ba

Ministan Harkokin Wajen Iran ne ya bayyana hakan inda ya ce "babu abin da zai sake komawa kamar da.

Iran ta bayyana cewa dole kasashen yankin su tabbatar da tsaron yankin ba tare da taimakon sojojin kasashen waje ba.

Ministan Harkokin Wajen Iran Abbas Araghchi ne ya bayyana hakan inda yace cewa “babu abin da zai sake komawa kamar a cen baya” bayan yakin zalunci Amurka da Isra’ila akan Iran.

Ya yi wadannan kalaman ne a bikin kafa cibiyar tattara bayanai da gidan tarihin da aka keɓe ga jami’in diflomasiyyar da ya yi shahada Kamal Kharrazi, wanda aka kashe a farkon wannan shekarar a wani harin ta’addanci na Amurka da Isra’ila.

Ya yi ikirarin cewa an sami sauye-sauye na asali da dabaru a Yammacin Asiya kuma babu abin da zai sake zama kamar da bayan yaƙin kwanaki 40 da ake shafe ana yi da Iran.

Dole ne mu fahimci cewa, Hanyoyin jigilar kaya da ke ratsa mashigar Hormuz ba za su sake zama kamar da ba, kuma ba za a sake sarrafa mashigar kamar yadda take a da ba.”

Iran ta takaita zirga-zirga ta mashigar Hormuz don mayar da martani ga mummunan harin da Amurka da Isra’ila suka kai a ranar 28 ga Fabrairu.

Bugu da kari, Araghchi ya jaddada cewa idan masu kai hari suka yi aiki da hankali, ba za su sake yin wani harin soja kan al’ummar Iran ba, yana mai cewa, “Sun gwada shi sau biyu, kuma sun ga sakamakon.”

Ya kamata Iran da ƙasashen yankin su zauna cikin kwanciyar hankali, ba tare da tsoma baki daga ƙasashen waje ba. “Wannan ita ce hanya ɗaya tilo ta cimma zaman lafiya, tsaro, da kwanciyar hankali a yankinmu,” in ji

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted