Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran ya bayyana cewa: Iran ba ta taɓa barin teburin tattaunawa ba, iyaka dai matsalar tana cikin dagewar da Amurka ta yi ne kan buƙatunta na bangare guda
Mai magana da yawun Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran Isma’il Baqa’i ya shaida wa gidan rediyon Jamus na ARD cewa: “Iran ba ta taɓa kauracewa teburin tattaunawa ba. A lokaci guda, tana shirye tsaf don kare yankin kasarta daga wuce gona da iri. Sannan ana isar da saƙonni ta hanyar masu shiga tsakani.”
Ya ƙara da cewa: “Amma matsalar tana cikin dagewar da Amurka ta yi kan buƙatunta na bangare guda. Iran ba ta da alaƙa da ayyukan da suke iƙirarin an yi a kan sansanonin jiragen sama a Ingila.”
Ya nuna cewa mashigar Hormuz ba ta da tsaro, ba wai Iran ce ta sanya ta zama mara tsaro ba, amma saboda Amurka da Haramtacciyar kasar Isra’ila suke yin amfani da wannan hanyar ruwa. Suna ci gaba da amfani da yankin gaba ɗaya don ƙaddamar da hare-haren soja da kuma ci gaba da aikata laifukan da ba su dace ba da kuma zalunci a kan Iran.
Baqa’i ya jaddada cewa: “Saboda haka, matuƙar wannan yanayi ya ci gaba, Iran ba ta da wani zaɓi illa ta ɗauki matakan da suka dace don kare mutuncin yankinta, tsaron ƙasa da kuma mutanenta.”