Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran ya gana da tawagar kwamandojin sojojin sama da na tsaron sararin samaniyar kasar
Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya gana da wata tawagar kwamandojin sojojin sama da na tsaron sararin samaniyar kasar na sojojin Jamhuriyar Musulunci ta Iran a safiyar yau Juma’a a daidai lokacin da ake gudanar da bukukuwan tunawa da kwanaki goma na samun nasarar juyin juya halin Musulunci.
Taron na yau ya zo daidai da zagayowar kwanaki goma na samun nasarar juyin juya halin Musulunci, kuma taron tunawa da mubaya’a mai dimbin tarihi ga Imam Khumaini (Allah ya kara masa yarda) a ranar 8 ga watan Fabrairun shekara ta 1979. Don haka a safiyar yau Juma’a Jagoran juyin juyahalin Musulunci Sayyed Ali Khamenei ya gana da wata tawagar kwamandojin sojojin sama da na tsaron sararin samaniya , inda suka tattauna muhimman batutuwan da suka shafi harkokin tsaron kasa.