Jagora: Siyasar Kasar  Iran  Ta Ginu Ne Akan Kyautata Alaka Da Kasashen Makwabta

Jagoran juyin musulunci na Iran Ayatullah sayyid Ali Khamnei wanda ya gana da sarkin Katar  a jiya Laraba ya bayyana cewa; Siyasar Iran ta ginu

Jagoran juyin musulunci na Iran Ayatullah sayyid Ali Khamnei wanda ya gana da sarkin Katar  a jiya Laraba ya bayyana cewa; Siyasar Iran ta ginu ne akan kyautata alaka da kasashen makwabta, kuma tuni an cimma sabbin matakai a wannan fagen.

Ayatullah Sayyid Ali Khamnei ya kuma fada wa sarkin na Katar Tamim Bin Hamad ali-Sani cewa, ministan harkokin wajen Iran Abbas Arakci yana fadi tashi a wannan fagen na kyautata alaka da kasashen makwabta, tare da yin kira da cewa yarjeniyoyin da aka kulla su zama masu kare maslahar kasashen biyu.

Ayatullah Sayyid Ali Khamnei ya bayyana kasar Katar a matsayin kasa abokiya, kuma ‘yar’uwa ta Iran, duk da cewa har  yanzu da akwai wasu batutuwa da ba a kai ga warware sub a,kamar dawo da kudaden Iran da aka zuba a Bankunan kasar daga Korea Ta Kudu.

A nashi gefen sarkin Katar ya jinjinawa matakan da Iran din take dauka na taimakawa raunana a duniya, da kuma al’ummar Falasdinu, kuma yadda ta kasance a tare da Falasdinawa wani abu ne da ba za taba mancewa da shi ba har abada.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments