Jagora: Musulunci Ya Daukaka Mata Matukar Dauka

Jagoran juyin juya halin musulunci Imam Sayyid Aliyul Khaminae ya bayyana cewa addinin musulunci ya daukaka matsayin macce ya kuma bada matsayin guda da maza

Jagoran juyin juya halin musulunci Imam Sayyid Aliyul Khaminae ya bayyana cewa addinin musulunci ya daukaka matsayin macce ya kuma bada matsayin guda da maza a fagagen zamantakewa da siyasa, ya kuma yi watsi ya akidar kasashen yamma wadanda suka kaskasntata suka maida ita kayan aika don cimma bukatatun wasu.

Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Jagoran yana fadar haka a wani jawabin da ya gabatar a taron dubban mata daga yankunan daban daban na kasar a yau laraba a nan Tehran.

Imam Khaminae ya ce, mata a Iran suna koikoyon Fatimah Azzahra (s) diyar manzon Allah (s) don haka suka kama hanyar daukaka wanda alah ya bawa mata. Fatima (s) makaranta ce ga mata kuma daukaka ce a garesu.

Imam Khaminae ya ce aladun kasashen yamma da kuma tsarin jarin hujja dangane da mata ba amintaccene a addinin musulunci ba. Yace tsare-tsaren da addinin musulunci ya zo da su na, hijabi da hana cakudar mata da maza a tarurruka, da kudaitar da aure da sauransu duk don kare Martaban mata ne a mataki na farko. Yace musulunci bai hana mata shiga a dama da su a cikin al-amuran zamantake da siyasa da sauransu ba, amma tare da kiyaye mutuncinta, da aikita na asali wanda shi ne kula da iyala da tarbiyyan yayanta.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments