Jagora: Muhimmin Aikin Makarantar “Hauza” Shi ne Isar Da Sakon Addini

Ayatullah Sayyid Ali Khamnei wanda ya aike da sako zuwa wurin taron tunawa da cikar  shekara 100 daga kafuwar cibiyar koyar da addinin musulunci ta

Ayatullah Sayyid Ali Khamnei wanda ya aike da sako zuwa wurin taron tunawa da cikar  shekara 100 daga kafuwar cibiyar koyar da addinin musulunci ta “Hauza” wanda aka yi a yau a birnin Kum, anan Iran, ya bayyana cewa: Aiki mafi muhimmanci na makarantar addini shi ne isar da sakon addinin musulunci domin gina sabon ci gaba na addinin musulunci.

Jagoran juyin musuluncin na Iran ya kuma bayyana cewa da akwai ayyuka masu yawa da suke na cibiyar koyar da addinin musulunci ta Hauza ne da sun kunshi bayar da jawabi akan sabbin batutuwa na zamani da suke bijirowa,  ruhin ci gaba, tsarkake zukata, da kuma siffa ta juyin juya hali.”

Ayatullah Sayyid Ali Khamnei ya kuma bayyana cewa daga cikin ayyukan cibiyar ilimin ta Hauza da akwai Shata muhimman layukan da za a gina ci gaban musulunci na zamani akansu, da kuma isar da sakwanninsa a cikin al’umma, kamar kuma yadda aikin Hauzar ne ta yi  tarbiyyar mutane su zama masana.

Tun da fari, Ayatullah Sayyid Ali Khamnei ya fara da bijiro da takaitaccen tarihin kafuwar cibiyar koyar da addinin musulunci ta Hauza a Kum, da rawar da Ayatullah Haj Sheikh Abdulkarim Ha’iri ya yi, har zuwa lokacin da ta rika bunkasa da ci gaba.

Jagoran juyin musuluncin na Iran ya bayyana Imam Khumaini ( q.s) a matsayin daya daga cikin malaman da Hauza ta haskaka da su, wanda ya yi nasarar kawo karshen tsarin sarauta na maha’inta.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments