Jagoran juyin juya halin musulunci na Iran, Ayatullah Sayyid Ali Khamnei ya bayyana cewa; makiya sun nufin rusa tsarin jamhuriyar musulunci ne ta hanyar mamaye wannan yankin da suke yi.
A lokacin da yake gabatar da jawabi a wurin taron karawa juna sani akan shahidan “Kare Haram’ da kuma kawancen gwagwarmaya, wanda aka yi a ranar 19 ga watan Yuni, wanda aka watsa cikakken bayanin a jiya 29 ga wannan watan ya bayyana cewa;
“Wadanda su ka kare kare haram da hubbare masu tsarki, sun sanar da wani yanayi mai jan hankali da ban mamaki, kuma yana a matsayin daya daga cikin albarkacin jamhuriyar musulunci ia Iran.
Jagoran juyin musuluncin na Iran ya bayyana cewa, yadda matasa da samari daga kasashe mabanbanta su ka je kare hubbare masu tsarki, ya tabbatar da cewa, bayan shekaru 40 daga cin nasarar juyin musulunci, tana da karfin samar da kumaji da gwagwarmaya kamar yadda ya kasance a farkon cin nasarar juyin musulunci.
Jagoran juyin musuluncin na Iran ya kuma ce, ya zama wajibi aikin da masu kare Haram su ka yi, ya isa ga ma’abota rayayyen lamiri a duniya.