Jagora: Ma’aikata Su Ne Jari Mafi Girma Domin Cimma Manufar Bunkasa Tattalin Arziki

Jagoran juyin musulunci na Iran Ayatullah Sayyid Ali Khamnei  ya fada a yau Asabar cewa: Ma’aikata ne jari mafi muhimmanci na samun zaman lafiya a

Jagoran juyin musulunci na Iran Ayatullah Sayyid Ali Khamnei  ya fada a yau Asabar cewa: Ma’aikata ne jari mafi muhimmanci na samun zaman lafiya a cikin al’umma da kuma cimma manufar sunan da aka bai wa wannan shekarar na : “Zuba Hannun Jari Domin Yin Kere-Kere.”

Ayatullah Sayyid Ali Khamnei wanda ya gana da ma’aikata da su ka fito daga sassan Iran, ya yi ishara da sake bude kamfanoni da dama a zamanin shugabancin Shahid Ra’isi, alhali gabaninsa an rufe su,tare da bayyana hakan da cewa daya ne daga cikin ayyukan da Shahidin ya aiwatar.

Jagoran juyin musuluncin na Iran ya kuma bayyana ma’aikatar da cewa, su nekashin bayan kowace al’umma, yana kuma mai yin addu’ar Allah ya ba su dacewa a cikin ayyukan da su ka Sanya a gaba.

Ayatullah Sayyid Ali Khamnei ya kuma ishara da cewa bude kasa domin shigo da haja abu ne mai sauki, amma a lokaci daya yana karya kasa, don haka abinda ya zama wajibi shi ne a kare yin kere-kere daga cikin gida.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments