Jagora : Kokarin Makiya Na Haifar Da Sabani Ya Ci Tura

Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya bayyana cewa kokarin da makiya suke yi na haifar da sabani a tsakanin

Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya bayyana cewa kokarin da makiya suke yi na haifar da sabani a tsakanin al’ummar kasar ta hanyar yi musu barazana ya ci tura.

Babban tattakin da al’ummar kasar suka yi a ranar 10 ga watan Fabrairu ya nuna cewa barazanar makiya ba ta da wani tasiri a kan wannan kasa da kuma al’ummarta.

Jagoran ya yi ishara da irin gagarumar fitowar al’ummar kasar a cikin jerin gwano da bukukuwan tunawa da cika shekaru 46 da juyin juya halin Musulunci, wanda ya hambarar da azzalumar gwamnatin Pahlavi ta tsohuwar gwamnatin Amurka.

Ayatullah Khamenei ya sake ba da misali da irin dimbin abubuwan da suka faru a lokacin zagayowar nasarar juyin juya halin Musulunci a wannan shekara.

Bayan shekaru arba’in da cin nasarar juyin juya halin Musulunci, a daidai lokacin da ake tunawa da nasarar juyin juya halin Musulunci, dukkanin al’ummar kasar, sojoji, jami’ai, sun fito duk kuwa da irin matsalolin da ake fuskanta.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments