Jagora : Gaza Ta Durkusar Da Gwamnatin Isra’ila Dake Samun Goyan Bayan Amurka

Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya ce karamin yankin Gaza ya durkusar da gwamnatin Isra’ila duk da makaman da ta ke

Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya ce karamin yankin Gaza ya durkusar da gwamnatin Isra’ila duk da makaman da ta ke dasu da kuma cikakken goyon bayan Amurka.

Ayatullah Khamenei ya ci gaba da cewa : tsayin daka da aka fara a Iran din, ya jawo farkawar wasu al’ummar musulmi kuma durkusar da Isra’ila a Gaza da Labanon misali ne.

Jagoran ya bayyana hakan ne a ranar Talata yayin wata ganawa da jakadun kasashen musulmi a birnin Teheran, a daidai lokacin da ake gudanar da bukukuwan zagayowar ranar aiko da sakon annabta ga Manzon Allah Muhammad (SAW).

Jagoran ya ce “A yau, bayanin da muke bayarwa na mulkin mallaka da girman kai yana bayyana gaba daya daga gwamnatin Amurka.

Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin dubban Falasdinawan Gaza suka fara komawa yankin bayan cimma yarejejeniyar tsagaita wuta da Isra’ila.

Ofishin yada labarai na gwamnati a zirin Gaza ya sanar da cewa Falasdinawa kusan 350,000 da suka rasa matsugunansu ne suka koma gida a gabar tekun a ci gaba da aiwatar da yarjejeniyar.

“Wannan ya zo ne bayan kwanaki 470 na kisan kiyashi da sojojin mamaya na Isra’ila suka yi,” wanda ya yi sanadin shahadar Falasdinawa sama da 47,000 tare da wargaza yankin.

An bayyana cewa sama da kashi 90%, na yankin ya lalace sakamakon hare haren Isra’ila wandanda suka ruguza duk wasu wurare da cibiyoyi masu matukar mahimmanci na Zirin kama daga asibitoci, makarantu, gidajen jama’a wuraren samar da ruwan sha da wutar lantarki.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments