Jagora: Allamah Na’ini Ya Kasance Ma’abocin Ilimi Da Sanin Siyasa

Jagoran juyin juya halin musulunci na Iran wanda ya gana da tawagar masu shirya taron tunawa da Alamah Mirzai Na’ini ( R.A), ya ce; muhimman

Jagoran juyin juya halin musulunci na Iran wanda ya gana da tawagar masu shirya taron tunawa da Alamah Mirzai Na’ini ( R.A), ya ce; muhimman siffofi biyu da malamin ya kebanta da su, su ne kirkira a fagen ilimi da kuma a cikin ilimin siyasa.

Ayatullah Sayyid Ali Khamnei ya bayyana Allamah Na’ini a matsayin daya daga cikin fitattun malamai, masu tarin sani a cbiyar ilimin addinin musulunci ta Hauza dake Najaf mai tsohon tarihi; jagoran juyin na Iran ya yi ishara da yadda marigayin malamin ya samar da ka’idojin da aka gina ilimin usulu akansu, wanda ya kai ga sabunta shi.

Daga cikin rukunonin tunanin Allamah Na’ini kamar yadda jagoran juyin ya ambata da akwai batun kafa tsarin musulunci akan ginshikin wilaya domin kalubalantar kama-karya, haka nan kuma ya yi Imani da cewa wajibi ne dukkanin jami’an gwamnatin su zama ana bibiyar ayyukan da suke yi da sa ido akansu.

Allamah Na’ini ya yi Imani da kafuwar hukumar musulunci wacce al’umma za su lamunta da ita, da hakan yake nufin tsarin jamhuriyar musulunci.

Allamah Na’ini ya rayu a karni na 19 miladiyya, ya kuma taka rawa wajen yunkurin rubuta tsarin Mulki a Iran wanda ya kayyade iko maras iya da sarki yake da shi.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted