Iyalan Malcolm X sun nemi Trump da ya yi bayani kan makomar batun kisansa

Iyalan Malcolm X, bakar fata fata kuma daya daga cikin jagororin  musulmin Amurka da aka kashe a ranar 21 ga Fabrairun 1965, sun bukaci shugaban

Iyalan Malcolm X, bakar fata fata kuma daya daga cikin jagororin  musulmin Amurka da aka kashe a ranar 21 ga Fabrairun 1965, sun bukaci shugaban Amurka Donald Trump da ya bayyana bayanan da ke da alaka da kashe shi, kamar yadda shafin Arabi 21 ya ruwaito.

Iyalan Malcolm X sun gabatar da bukatar ne a cikin wata sanarwa da Ben Crump, lauya mai kare hakkin bakar fata a Amurka ya bayar, a wani taro da aka gudanar tare da iyalan Malcolm X a birnin New York na kasar Amurka domin cika shekaru 60 da kashe shi.

Crump, ya yi nuni da wani umarni da Trump ya sanya wa hannu a watan Janairu, inda ya bayyana dukkan bayanan da suka shafi kisan gillar John F. Kennedy, da Martin Luther King, Jr., inda ya bukaci Trump da ya bayyana duk wasu bayanai da suka shafi kisan Malcolm X.

Crump ya bayyana fatansa na cewa Trump zai amsa bukatun iyalan Malcolm X. “Muna sa ran Trump zai dauki mataki a ranar 19 ga Mayu, 2025, a bikin cika shekaru 100 da haihuwar Malcolm X,” in ji shi.

A ranar 19 ga Mayu kowace shekara, Amurkawa da yawa suna bikin “Ranar Malcolm X” don girmama shi a  matsayin daya  daga cikin fitattun masu fafutukar kare hakkin bakar fata a Amurka a cikin shekarun 1960.

Malcolm X ya kasance kwararre wajen Magana da kaifin basira da kuma kwarjini. Amurkawa da dama sun kadu a lokacin da labarin kisansa ya yadu a shekara 1965.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments