Da safiyar Yau Laraba ne sojojin Haramtacciyar kasar Isra’ila su ka kai hare-hare a yankuna daban-daban na zirin Gaza, tare da rushe gidaje da dama. Sojojin mamayar sun yi amfani da jiragen sama marasa matuki da kuma tankokin yaki domin rushe gidajen. A arewacin Gaza da gabashin Jabaliya sojojin na mamaya sun yi amfani da manyan bindigogi akan gidajen fararen hular. A unguwar “Tuffah” ma an ga yadda sojojin mamayar su ka aike da jiragen yaki marasa matuki.
A can kudancin Gaza kuwa jiragen yakin Haramtacciyar Kasar Isra’ila ne su ka kai hare-hare akan barin Bani-Suhaila a gabashin Khan-Yunus,a lokaci daya kuma manyan bingigoginsu su ka bude wuta akan iyaka.
Tun bayan da aka tsagaita wutar yaki a cikin watan Oktoba ne, Sojojin mamayar Haramtacciyar Kasar Isra’ilan suke ci gaba da kai hare-hare akan Gaza ba tare da kakkautawa ba. Daga tsagaita wutar zuwa yanzu adadin Falasdinawan da su ka yi shahada a sanadiyyar hare-haren na ‘yan sahayoniya sun haura 300.
Hukumar agaji a yankin na Gaza ta yi gargadi akan cincirindon ‘yan hijira da suke rayuwa a cikin hemomin da babu kayan da rayuwa take da bukatuwa da su domin ci gaba. Ruwan sama yana ci gaba da sauka a yankuna mabanbanta na Gaza da sanyi yake karuwa ba tare da samar da na’urorin dumama hemomin ba.