Gwamnatin mamayar haramtacciyar kasar Isra’ila sun fito fili sun amince da na’urorin da sojojin Yemen suke amfani da su wajen harba makamai masu linzami, inda makaman suke ratsa cikin tsarin tsaron sararin samaniyar Isra’ila tare da kai munanan hare-hare kan duk wurin da suka saita su a cikin haramtacciyar kasar ta Isra’ila, ba tare da nasarar kakkabo makaman ba.
Kakakin sojojin mamayar haramtacciyar kasar Isra’ila ya bayyana cewa: Sojojin saman mamayar Isra’ila sun kasa kakkabo wani jirgin saman yakin Yemen masar matuki ciki da ya kawo hari kan yankin Yavnah dake kudancin birnin Tel Aviv a jiya litinin.
‘Yan sa’o’i kadan bayan sanarwar da kakakin rundunar sojin kasar Yemen Birgediya Janar Yahya Saree ya fitar, dakarun makiya yahudawan sahyoniya sun sanar da karin bayani game da harin da sojojin Yamen suka kai kan wani muhimmin hari a birnin Tel Aviv.
A cikin wata sanarwa da majiyar sojojin mamayar Isra’ila ta fitar ta bayyana cewa: Jirgin saman yakin Yemen maras matuki ciki ya kutsa cikin sararin samaniyar Isra’ila, kuma babu wata Alamar ya shigo ballantana a kunna na’urar gargadi kamar yadda aka saba idan aka kawo hari domin jama’a su shige cikin maboyar karkashin kasa.