Bayanai daga falasdinu na cewa an kashe Hamas Abdul-Latif al-Qanou wani kakakin kungiyar Hamas a wani harin da Isra’ila ta kai a arewacin Gaza.
Kamfanin dillancin labaran Quds na Falasdinu ya bayar da rahoton cewa, jami’in ya yi shahada ne a wani harin da Isra’ila ta kai ta sama a kan tantinsa a garin Jabalia da ke arewacin zirin Gaza.
Har ila yau harin ya yi sanadin jikkatar mutane da dama da suka hada da kananan yara.
Wannan kisan dai shi ne na baya bayan nan a jerin hare-haren wuce gona da irin da gwamnatin Isra’ila ke ci gaba da yi a zirin Gaza tun a watan Oktoban shekarar 2023, bayan wani dan takaitaccen lokaci inda ta saba ka’idojin tsagaita bude wuta da kungiyar Hamas, tare da kai munanan hare-hare.
Shahadar al-Qanou ta zo ne kwanaki kadan bayan kisan gillar da gwamnatin sahyoniyawan ta yi wa wasu fitattun jami’an ofishin siyasa na Hamas, wato Ismail Barhoum da Salah al-Bardaweel. An kashe su duka a samame daban-daban.
A baya-bayan nan dai babban mai magana da yawun kungiyar Hamas Sami Abu Zuhri ya jaddada cewa kisan gilla ba zai hana kungiyar ci gaba da fafutukar kwato yankunan Falasdinawa ba.