Search
Close this search box.

Isra’ila Ta Sake Kaddamar Da Wasu Munanan Hare-Hare A Gabashin Gaza

Isra’ila ta kai wasu sabbin jeri hare-hare a Birnin Gaza, inda ta kashe gomman Falasdinawa fararen hula, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Falasɗinawa WAFA

Isra’ila ta kai wasu sabbin jeri hare-hare a Birnin Gaza, inda ta kashe gomman Falasdinawa fararen hula, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Falasɗinawa WAFA ya bayyana, inda yace an samu rahotannin jikkata mutane daga yankunan Sheikh Radwan da Shujaeya da kuma gabashin Birnin Gaza.

Tun da farko, Isra’il ta kashe akalla fararen hula 12, ta kuma jikkata wasu a hare-haren jiragen sama a Deir al Balah a tsakiyar Gaza da aka mamaye, kamar yadda WAFA ya rawaito.

Wakilin WAFA ya ce an kai gawawwakin mutane 12 Asibitin Shahidai na Al-Aqsa a Deir al Balah bayan hare-haren sama kan gidan iyalen Eslayyim a birnin.

Isra’ila ta kuma kashen wasu fararen hular uku a yankin Al-Mansura a unguwar Shejaiya, da wasu ukun kuma daban a yammacin Rafah, a cewar kamfanin dillnacin labaran.

Hukumomin lafiya sun shaida wa WAFA cewa daga wayewar gari an kai aƙalla gawawwakin fararen hula 31 asibitocin yankin.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Inline Feedbacks
View all comments