Isra’ila ta katse wutar lantarki a zirin Gaza

Gwamnatin Isra’ila ta sanar da katse wutar lantarki a Zirin Gaza. Ministan Makamashi na Isra’ila Eli Cohen ne ya sanar da matakin da gwamnatin kasar

Gwamnatin Isra’ila ta sanar da katse wutar lantarki a Zirin Gaza.

Ministan Makamashi na Isra’ila Eli Cohen ne ya sanar da matakin da gwamnatin kasar ta dauka na katse wutar lantarki a zirin, a yayin da wasu rahotanni ke cewa mataki na gaba bayan katsewar wutar lantarkin, shi ne yanke ruwa a arewacin zirin Gaza.

Ya ce matakin da gwamnatin kasar ta dauka na kara kaimi ne domin kwato dukkan mutanen da ake garkuwa dasu tare da tabbatar da cewa Hamas ba za ta ci gaba da zama a Gaza ba bayan yakin.

A daya banagaren kuma Ministan kudi na Isra’ila ya yi ikirarin cewa gwamnatin kasar za ta hada kai da gwamnatin Amurka karkashin jagorancin Donald Trump domin sanin kasashen da za su karbi bakoncin bakin haure daga Gaza.

A baya-bayan nan ne shugaban Amurka Donald Trump ya gabatar da shirin tilastawa mazauna yankin Zirin Gaza zuwa kasashen Jordan da Masar da ke makwabtaka da ita.

Shugaban Masar Abdel Fattah al-Sisi da Sarkin Jordan Abdallah na biyu sun yi kakkausar suka ga shirin mamayar tare da jaddada cewa ba za su iya karbar sabbin ‘yan gudun hijira ba.

Jami’an kasashen Jordan da Masar da kuma wasu kasashen Larabawa sun jaddada cewa dole ne a kafa kasar Falasdinu, kuma a bar al’ummarta su zabi makomarsu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments