Isra’ila Ta Kashe Mutane 4 Tare Da Jikkata Wasu Guda 3 A Kudancin Labanon

A ci gaba da keta yarjejeniyar dakatar da bude wuta da HKI ke yi a kasar labanon a jiya ma ta kai hari a kudancin

A ci gaba da keta yarjejeniyar dakatar da bude wuta da HKI ke yi a kasar labanon a jiya ma ta kai hari a kudancin kasar kuma ta yi sanadiyar  mutuwar mauta 4 tare da jikkata wasu guda 3,

Isra’ila ta kai hari da jirgin sama mara matuki kan wata mota a kauyen kafr rumman , kana kuma ta sake kai wani harin a garin kafr sir kamar yadda rahotanni suka bayyana, kuma wadannan hare haren suna zuwa ne kwanaki 3 bayan da sojojin israila suka kai samame ta kasa a kudancin labanon a yankin Nabatiya inda suka kai hari a jiya,

A ranar jumaa da ta gabata ne shugaban kasar ta labanon  joseph Aun ya nuna damuwarsa game da ci gaba da keta yarjejeniyar dakatar da bude wuta da Isra’ila ke yi, inda yayi tir da tel aviv game da irin mataken  da take dauka na karya yarjejeniyar.

A yan kwanankin nan sakatare janar din kungiyar hizbullah na kasar labanon shaikh Naim Qassem  ya jaddada cewa tsayin daka ne karfin labanon, don haka Amurka na matsin lamba ne don ganin an danneta an tauye mata yanci da raunata ta don biyan muradun gwamnati.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments