Hukumar kare fararen hula a Gaza ta ce wasu hare-haren Isra’ila sun kashe Falasdinawa shida a Gaza.
Kakakin hukumar Mahmoud Bassal, ya ce an kashe Falasdinawa hudu tare da jikkata wasu da dama a wani harin sama da Isra’ila ta kai a kudu maso yammacin sansanin ‘yan gudun hijira na Bureij da ke tsakiyar Gaza.
Asibitin Shahidai na Al-Aqsa da ke kusa da Asibitin Al-Awda kowannensu ya tabbatar da samun gawawwaki biyu bayan harin.
Hukumar ta kuma ce an kashe Bafalasdine guda a wani harin jirgi mara matuki da Isra’ila ta kai kan wani tanti a sansanin al-Munasara na mutanen da suka rasa matsuguni a Deir al Balah.
Wani hari na jirgi mara matuki da aka kai a arewacin sansanin ‘yan gudun hijira na Nuseirat, wanda shi ma yake a tsakiyar Gaza, ya kashe wani mutum, in ji hukumar.
Asibitin Shahidai na Al-Aqsa ya tabbatar da karbar gawawwaki biyu bayan wadannan hare-haren.
Fiye da Falasdinawa 1,600 ne aka kashe tun lokacin da aka fara tsagaita wuta, a cewar wasu alkaluman AFP da ya dogara da bayanai daga Ma’aikatar Lafiya ta Gaza.