Isra’ila Ta Kashe Falasdinawa 62 Duk Da Yarjejeniyar Tsagaita Wuta

Yayin da masu shiga tsakani ke aiki a Qatar domin daddale yarjejeniyar tsagaita bude wuta, sojojin Isra’ila sun kashe Falasdinawa akalla 62 a hare-haren da

Yayin da masu shiga tsakani ke aiki a Qatar domin daddale yarjejeniyar tsagaita bude wuta, sojojin Isra’ila sun kashe Falasdinawa akalla 62 a hare-haren da suka kai a Gaza.

A cewar rahotanni da ke fitowa daga Gaza a ranar Laraba, ‘yan jarida biyu na cikin wadanda abin ya shafa.

A cikin wata sanarwa da hukumar kare hakkin fararen hula ta Gaza ta fitar ta ce an kawo gawarwaki 11 a asibitin shahidan Al-Aqsa da ke tsakiyar Gaza bayan da sojojin Isra’ila suka kai hari a wani gidan iyali dake Deir al-Balah cikin dare.

 Wani yaro dan shekara bakwai da wasu matasa uku na daga cikin wadanda suka mutu.

A cewar hukumar, wani harin ya sake afkawa wani ginin makaranta da ake amfani da shi a matsayin mafaka ga Falasdinawa da suka rasa matsugunansu a birnin Gaza.

Harin ya kashe mutane bakwai tare da jikkata wasu da dama.

Harin na uku da asuba ya afkawa wani gida a sansanin ‘yan gudun hijira na Al-Nuseirat.

Hukumar ta ce an kashe mutane shida tare da jikkata bakwai.

Hukumar ta kara da cewa an kai hari na hudu a sansanin Shati da ke birnin Gaza tare da kashe mutane uku.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments