Rahotanni daga Falasdinu na cewa akalla Falasdinawa 61 ne sukayi shahada a cikin sa’o’i 24 da suka gabata, in ji ma’aikatar lafiya ta Gaza.
A cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Litinin, ma’aikatar ta ce an gano gawarwaki hudu a karkashin baraguzan gini, sannan an kwantar da mutane 134 da suka jikkata a asibiti cikin sa’o’i 24 da suka gabata.
Adadin wadanda suka mutu a zirin Gaza ya kai 50,082, yayin da mutane 113,408 suka samu raunuka tun bayan fara yakin kisan kare dangi na Isra’ila a ranar 7 ga Oktoba, 2023.
Har ila yau, a ranar litinin, sojojin Isra’ila sun kai harin bam a asibitin Nasser, mafi girma a kudancin Gaza, da ke Khan Younis, harin da ma’aikatar ta yi Allah wadai da shi a matsayin “laifi na yaki.”
A ranar 1 ga Maris, bayan karewar kashi na farko na yarjejeniyar tsagaita bude wuta, Isra’ila ta kaurace wa shiga shawarwarin kashi na biyu na yarjejeniyar.
Tun a ranar 18 ga watan Maris ne dai aka sake tada jijiyoyin wuya, lokacin da Isra’ila ta ci gaba da kai hare-hare, lamarin da ya karya yarjejeniyar tsagaita bude wuta da kuma musayar fursunoni.