Isra’ila Ta Kai Wa Sojojin MDD Hari A Kasar Lebanon

 Tankar yakin Haramtacciyar Kasar Isra’ila ta bude wuta akan dakarun zaman lafiya na MDD dake kudancin Lebanon Dakarun zaman lafiyar na MDD dake kudancin Lebanon

 Tankar yakin Haramtacciyar Kasar Isra’ila ta bude wuta akan dakarun zaman lafiya na MDD dake kudancin Lebanon

Dakarun zaman lafiyar na MDD dake kudancin Lebanon (UNIFiL) sun sanar da cewa tankar yakin “Isra’ila” ta buder wuta akansu, da hakan ya tilasta musu guduwa zuwa inda za su buya.

Rundunar ta “UNIFIL” ta kuma bayyana abinda ya faru da cewa keta kudurin MDD ne mail amba 1701, tare da yin kira ga “Isra’ila’ da ta dakatar da abinda take yi.

Wannan dai ba shi ne karon farko ba da Haramtacciyar Kasar Isra’ila take keta kudurin MDD ta hanyar kai hare-hare da kuma yin kutse a cikin yankunan dake kan iyaka.

A ranar 27 ga watan Oktoba ma dai rundunar ta MDD ta sanar da cewa ta harbo wani jirgin sama maras matuki na Haramtacciyar Kasar Isra’ila da ya rika shawagi akan sojojinta masu sintiri da zummar kai musu hari. Haka nan kuma a waccan ranar wani jirgin  saman maras matuki na “Isra’ila” ya jefa bom a kusa da dakarun a garin Kafar-kalla.

A baya a ranar 12 ga watan Oktoba wani jirgin na “Isra’ila” da ya jefa bom, ya jikkata daya daga cikin dakarun zaman lafiyar na MDD.

An kafa rundunar UNFEL ne dai a 1978 bayan da sojojin Haramtacicyar Kasar Isra’ila su ka kutsa cikin kudancin Lebanon, an kuma karfafa ayyukan rundunar a 2006 da fitar da kuduri 1701. Da akwai sojoji 10,000 akarkashin wannan rundunar domin sa ido akan dakatar da yaki daga Isra’ila da kuma karfafa sojojin Lebanon a kudancin tafkin “Litani”.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments