Isra’ila ta sake kai wasu sabbin hare-hare a kasar Siriya, wadanda su ne na baya bayan nan data kai tun bayan faduwar gwamnatin Bashar Al-Assad.
Tun bayan lamarin Isra’ila ta fara kai hare-hare kan wurare da daman a Siriya musamman cibiyoyin soji da wuraren adana makamai.
Sama da hare-hare 60 Isra’ila ta kai a cikin ‘yan sa’o’i kadan kan wuraren soji a fadin kasar ta Syria, a baya baya nan kusan mako guda bayan kwace Damascus daga hannun gwamnatin Bashar al-Assad, in ji wata kungiya mai zaman kanta.
Kungiyar kare hakkin bil adama ta kasar Syria (SOHR) ta sanar da cewa, “An kai hare-hare 61 cikin kasa da sa’o’i biyar” da yammacin ranar Asabar da Isra’ila ta yi.
Kungiyar ta kara da cewa: “Isra’ila na ci gaba da zafafa hare-hare ta sama kan yankunan kasar Siriya.
Hare-haren da Isra’ila ta kai Siriya sun kai “446 tun bayan faduwar gwamnatin Bashar al-Assad.