Israila Ta Kai Hari  Kan Ofishin kungiyar UNICEF Dake Gaza A

Rahotanni sun bayyana cewa gwamnatin isra’ila na fuskantar suka game da matakin da ta dauka na kai hari kan kungiyar unicef ta majalisar dinkin duniya

Rahotanni sun bayyana cewa gwamnatin isra’ila na fuskantar suka game da matakin da ta dauka na kai hari kan kungiyar unicef ta majalisar dinkin duniya a gaza, matakin da falasdinawa da masu sa ido ke gani a matsayin wata dabara ta murukushe kungiyoyin agaji da kuma fitar da kungiyoyin majalisar dinkin duniya daga yankin gaza

Rahoton da wani jami’in majalisar dinkin duniya ya fitar a jiya jumaa ya nuna cewa sojojin isra’ila sun kama wani ma’aikacin UNICEF mai suna Raed Afif mai shekaru 45 da haihuwa a kerem shalom alokacin da yake gudanar da ayyukansa.

Yazu wa yanzu isra’ila bata bayyana dalilan da suka sanya ta kama shi ba kuma take ci gaba da tsare shi.

Kwana daya kafin tayi kamun isra’ila ta bukaci kungiyar ta Unicef da ta kwashe dukkan kayayyakin agajinta daga yankin , kawai sai ta rufe dukkan kofofin shiga da magunguna zuwa asibitocin dake arewacin yankin Gaza. Kungiyoyin bada agaji na duniya sun yi gargadin cewa wannan matakin an dauke shi ne domin yanke duk wasu ayyukan jinkai da ake yi da kuma korar dukkan kungiyoyin agaji da hakan zai kara sanyawa yanayi ya kara tazzar a yankin Gaza.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted