Isra’ila Ta Kai Hare-hare A Kudancin Syria

Jiragen yakin Isra’ila sun kai hare-hare da dama a kan wasu sansanonin soji a kudancin kasar Siriya, ciki har da wasu yankunan da ke wajen

Jiragen yakin Isra’ila sun kai hare-hare da dama a kan wasu sansanonin soji a kudancin kasar Siriya, ciki har da wasu yankunan da ke wajen Damascus babban birnin kasar da kuma lardin Deraa da ke kudancin kasar.

Hare-haren dai ya biyo bayan kiran da firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya yi na karbe yankin kudancin Siriya baki daya.”

Jaridar Yedioth Ahronoth ta Isra’ila ta kuma bayar da rahoton cewa, Tel Aviv ta fara aiwatar da wani shiri na “shiga kudancin Syria.

Ministan tsaron Isra’ila, Israel Katz, ya ce jiragen yakin Isra’ila sun kai hare-hare a kudancin Syria a daren Talata, yana mai cewa harin wani bangare ne na sabuwar manufar Isra’ila ta “kawar da ayyukan soji a kudancin Syria.”

A cikin wata sanarwa da Katz ya fitar, ya ce harin wani bangare ne na manufar da firaminista Benjamin Netanyahu ya sanar a ranar Litinin, na “kawar da ayyukan soji kudancin Syria.”

Ya kara da cewa, za a tarwatsa duk wani yunkuri na dakarun sabuwar gwamnatin Syria da kungiyoyin ‘yan tawaye na kafa kansu a kudancin Syria.

A daya bangaren kuma, kafofin yada labaran kasar Syria sun rawaito cewa jiragen yakin Isra’ila sun kai hare-hare da dama a kudancin kasar ta Syria, yayin da sojojin kasa suka kutsa kai tsakanin Daraa da Quneitra dake kudancin kasar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments