Isra’ila ta kaddamar da hare-hare ta kasa a tsakiya da kudancin zirin Gaza

Rundunar sojin Isra’ila ta sanar a ranar Larabar nan da cewa, ta kaddamar da hare-hare ta kasa a tsakiya da kudancin zirin Gaza, biyo bayan

Rundunar sojin Isra’ila ta sanar a ranar Larabar nan da cewa, ta kaddamar da hare-hare ta kasa a tsakiya da kudancin zirin Gaza, biyo bayan hare-haren wuce gona da iri kan yankin Falasdinu.

Sanarwar ta bayyana cewa, sojojin sun karbe iko tare da fadada shi zuwa tsakiyar hanyar Netzarim, da nufin fadada yankin tsaro da samar da wani bangare na raba tsakanin arewaci da kudancin Gaza.

A halin da ake ciki kuma, ministan tsaron Isra’ila, Israel Katz, ya yi gargadin karshe ga Falasdinawa a zirin Gaza, inda ya bukaci da su sako Isra’ilawa da suke garkuwa da su, su kuma kawar da kungiyar Hamas, a cewar wata sanarwa daga ofishinsa.

“Idan ba a sako dukkan mutanen Isra’ila da aka yi garkuwa da su ba, kuma ba a kawar da Hamas gaba daya daga Gaza ba, Isra’ila za ta dauki matakan da ba a taba ganin irinta ba inji shi.

“Muna ba ku shawarar ku bi shawarar shugaban Amurka: ku saki mutanen da aka yi garkuwa da su, ku kawar da Hamas,” in ji Katz a wani faifan bidiyo na yaren Hebrew da ofishinsa ya fitar.

Firayi inistan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya ce ya umurci sojojin da su dauki ” mataki” kan Hamas a Gaza, yana mai zargin kungiyar da kin sakin fursunoni da rashin amincewa da shawarwarin Isra’ila kan tsagaita bude wuta.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments