Isra’ila Na Mamaye Yankunan Siriya Bayan Faduwar Gwamnatin Al-Assad

kafofin yada labarai sun bayar da rahoton cewa sojojin mamayar da sojojin gwamnatin sahyoniyawan ke yi a yankunan kasar Siriya tare da jibge sojoji a

kafofin yada labarai sun bayar da rahoton cewa sojojin mamayar da sojojin gwamnatin sahyoniyawan ke yi a yankunan kasar Siriya tare da jibge sojoji a Quneitra.

A sa’i daya kuma, Benjamin Netanyahu ya sanar da cewa, sojojin Isra’ila sun kwace wani yanki na tuddan Golan da yarjejeniyar tsagaita bude wuta da aka kulla da Syria a shekarar 1974 ta tanada.

Wata kafar yada labaran Isra’ila ta bayar da rahoton cewa, gwamnatin Isra’ila na ci gaba da hulda kai tsaye da kungiyoyin da ke dauke da makamai a kasar Siriya, ciki har da kungiyar Hayat Tahrir al-Sham (HTC) wacce ta kai farmakin da a karshe ya kai ga kwace babban birnin kasar Damascus da sanyin safiyar Lahadi.

Tashar talabijin ta Aljazeera ta sanar da cewa, a karon farko tun shekara ta 1974, motocin soji na gwamnatin sahyoniyawan sun shiga yankunan kudancin kasar Siriya.

Wasu kafafen yada labarai sun rawaito cewa yahudawan sahyoniya sun kutsa cikin zurfin kilomita 14 cikin kasar Siriya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments