Isra’ila na ci gaba da kai munanan hare-hare kan yankuna daban-daban a fadin kasar ta Siriya, yayin da mayakan da ke samun goyon bayan kasashen yammacin duniya, wadanda suka hambarar da gwamnatin kasar a farkon wannan wata, suka karfafa musu gwiwa.
A ranar Litinin, jiragen yakin Isra’ila sun kai hari kan muhimman wurare da kayayyakin aikin soji a gabar tekun yammacin kasar, ciki har da biranen Tartus da Latakia, inda suka yi luguden wuta kan sansanonin makamai masu linzami da ma’ajiyar harsasai.
An samu tashin bama-bamai masu yawa a garuruwan a lokacin hare-haren.
Tashar talabijin ta al-Mayadeen ta kasar Labanon ta ce sojojin mamaya na Isra’ila sun kuma kai hari a wani yanki mai nisan kilomita 15 a lardin Quneitra na yammacin kasar Siriya.
Kamfanin dillancin labaran Sputnik na kasar Rasha ya kuma bayar da rahoton hare-haren da Isra’ila ta kai kan cibiyoyin soji a Hama da Homs, wasu larduna biyu na yammacin kasar, inda ya kara da cewa hare-haren da aka kai kan Hama da Aleppo, wadanda ke a yammacin Syria, sun girgiza wuraren da aka kai harin kamar girgizar kasa.
A bangare guda, majiyoyin cikin gida sun bayar da rahoton cewa, jiragen yakin gwamnatin kasar sun kuma kai hari a filin jirgin saman soji da ke lardin Deir al-Zawr da ke gabashin kasar.