Isra’ila:  Makaman Hizbullah Masu Linzami Suna Nan Daram

Tsohon shugaban  hukumar  tsaro ta “Aman” Amus Malka ya bayyana cewa; Isra’ila ba za ta taba iya rusa barazanar da take fuskanta ba daga makamai

Tsohon shugaban  hukumar  tsaro ta “Aman” Amus Malka ya bayyana cewa; Isra’ila ba za ta taba iya rusa barazanar da take fuskanta ba daga makamai masu linzami ba.

Tsohon shugaban kungiyar leken asirin HKI ta cikin gida “Aman” ya kuma ce; Hizbullah suna da makamai masu linzami da za su iya harba 100 a kowace rana har tsawon watanni masu yawa, don haka tattaunawa ake bukata.

Malka wanda tashar talabijin ta 7 ta yi hira da shi ya kuma ce, muna da bukatar warware matsalar ta hanyar tattaunawa.

A  yau Talata kafafen watsa labarun na HKI  sun kuma bayyana cewa; Yankuna da Hizbullah take kai wa hare-hare suna karuwa, kuma ‘yan share wuri zauna ba a shirye suke su koma inda su ka baro ba.  A jiya Litinin kadai kungiyar ta Hizbullah ta harba makamai masu linzami 230 a sassa mabanbanta na HKI.

Share

5 1 vote
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments