Isra’ila da kungiyar Hamas sun amince da yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza da kuma sako mutanen da aka yi garkuwa da su, Qatar, daya daga cikin manyan masu shiga tsakani a tattaunawar ta tabbatar.
A cewar firaministan Qatar, tsagaitawar za ta fara aiki ne a ranar Lahadi 19 ga watan Janairu, inda za a sako wasu ‘yan Isra’ila 33 da aka yi garkuwa da su, da kuma sakin Falasdinawa kusan dubu daya da ake tsare da su a Isra’ila.
A matakin farko yarjejeniyar ta kuma tanadi janyewar sojojin Isra’ila a hankali daga tsakiyar zirin Gaza da kuma dawo da Falasdinawa yankinsu daga arewacin zirin inji Firaministan Qatar.
Duk da sanarwar da aka cimma, ofishin firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya ce har yanzu da sauran batutuwan “da za a warware” a cikin yarjejeniyar, amma yana fatan kammala su.
Netanyahu ya godewa zababben shugaban Amurka Donald Trump, da kuma shugaba mai barin gado Joe Biden.
A Isra’ila dai tuni aka fara yin watsi da yarjejeniyar tare da yin Allah wadai da ita.
Ministan masu tsatsauran ra’ayi Bezalel Smotrich ya yi tir da yarjejeniyar a matsayin “mai hadari” ga Isra’ila. “Yarjejeniyar da za a gabatar wa gwamnati mummunar yarjejeniya ce kuma mai hadari ga tsaron kasar,” in ji shi a cikin wata sanarwa.