Kafafen watsa labarun HKI sun ambaci cewa, Isra’ila tana fuskantar gajiyawa wajen fuskantar barazanar da take fuskanta daga Yemen.
Jaridar “Yediot Ahranot’ ta buga cewa; Makami mai linzamin da aka harbo daga Yemen ya yi barna mai girma a cikin filin wasan da ya sauka da kuma gine-ginen da suke kusa da shi.
Jaridar ta kara da cewa; Baki dayan wurin da makamin ya sauka ya ruguje, babu abinda bai tarwatse ba.
Har ila yau jaridar ta ce, baya ga rusa gine-ginen da makami mai linzamin ya yi, ya kuma jikkata mutane 30 da aka kai su asibiti.
Har iya yau kafafen watsa labarun na HKI sun ce, ko kadan Isra’ila ba ta tsinkayo za ta fuskanci hatsari har haka ba daga Yemen, don haka ba ta shirya ba, ta fuskar leken asiri da kuma siyasa, shi ya sa martanin da take mayarwa yake da rauni.
Miliyoyin Yahudawa ‘yan share wuri zauna ne su ka farka daga bacci a guje su ka nufi mabuya saboda fadowar makami mai linzamin daga Yemen.
Wasu da dama ma ba su sami damar isa ga mabuyar ba, kamar yadda kafafen watsa labarun su ka sanar.