Jaridar “Maariv” ta HKI ta buga rahoto wanda ya ambaci karfin sojan Iran sannan ta ce; Isra’ila ba ta da karfin da za ta yi cikakken yaki da Iran.
Rahoton ya cigaba da cewa, Iran wata kasa ce mai girma da ta mallaki dubban daruruwan makamai masu linzami, kuma tattalin arzikinta ya fi na Isra’ila karfi, don haka bai kamata a dauki Iraniyawa da sauki ba.
A baya janar Ishak Barik mai ritaya wanda ake kira sarkin Fushi a Isra’ila ya yi hira da tashar talabijin din ta 12, ya furta cewa; A halin da sojojin kasa na Isra’ila suke ciki a yanzu ba za su iya yin yaki a cikin fagage masu yawa a lokaci daya ba.
Janar Barik wanda shi ne kwamandan sojojin sa-kai na fararen hula a yanzu, ya kara da cewa, rundunonin sojojin nasu sun tsufa a yanzu, kuma sun kasa murkushe mayakan Hamas.