Isra’ila : An yi zanga zangar adawa da gwamnatin Netanyahu a Tel-Aviv

A Isra’ila dubban masu zanga-zanga ne suka taru a Tel Aviv domin nuna adawa da mulkin firaministan kasar Benjamin Netanyahu. Masu zanga zangar sun kuma

A Isra’ila dubban masu zanga-zanga ne suka taru a Tel Aviv domin nuna adawa da mulkin firaministan kasar Benjamin Netanyahu.

Masu zanga zangar sun kuma bukaci a tsagaita bude wuta da kuma sako fursunonin da ake tsare da su a Gaza.

Sun rike alluna masu dauke da hotunan wadanda  ake tsare da su a Gaza ko kuma allunan neman tsagaita bude wuta da Hamas cikin gaggawa.

Gamayyar kungiyoyin da ke adawa da shugaban majalisar ministocin ne suka shirya zanga-zangar da ta barke a makon da ya gabata, wanda suke zarginsa da matakin korar shugaban hukumar liken asiri ta cikin gida wato Shin Bet, Ronen Bar.

Wata Kuri’ar jin ra’ayin jama’a a isra’ila ta nuna cewa yawancin ‘yan Isra’ila na adawa da kawo karshen yarjejeniyar tsagaita bude wuta inda suke son ci gaba da tattaunawa da Hamas.

Kungiyar Hamas ta sake nanata cewa za a iya kashe mutanen da suka yi garkuwa da su idan Isra’ila ta yi kokarin kwato su da karfin tsiya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments