IRGC Ya Kaddamar Da Sabon Sansanin Jiragen Yaki Na Karkashiun Kasa

Janar Hussain Salami babban kwamandan dakarun kare juyin juya halin musulunci a nan Iran ya kaddamar da sabon sansanin jiragen yaki wadanda ake sarrafasu daga

Janar Hussain Salami babban kwamandan dakarun kare juyin juya halin musulunci a nan Iran ya kaddamar da sabon sansanin jiragen yaki wadanda ake sarrafasu daga nesa na karkashin kasa.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Janar Salami yana cewa, wadannan jiragen yakin da ake sarrafasu daga nesa, suna iya daukar hotunan jiragen yakin Amurka wadanda suka kasance sansanin jiragen saman yaki na kasar wadanda suke cikin tekuna, don amfani da hotunan saboda kai wa sansanin hare hare.

Salami yace gabatar da wannan sansanin gargadi ne ga mjakiya, sannan duk wata kasa a yankin wacce ta bar Amurka ta yi amfani da dandanin sojojinta da ke kasar don kaiwa kasar Iran hare0hare kasar ma ta zama filin daga.

Wannan kaddamarwan ta na zuwa ne bayan da kasashen Amurka da HKI suka yi barazanar farwa kasar don wargaza cibiyoyin Nukliyar kasar ta Iran. Sai daga bayan shugaba Trump yace ya fi son a cimma yarjeniya da Iran maimakon yaki.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments