Dakarun kare juyin juya halin musulunci na Iran sun sanar da gano da kuma rusa wata kungugun masu yi wa Amurka da Isra’ila leken asiri a yankin Arewacin Iran.
Kwamandan dakarun kare juyin juya halin musulunci a yankin Mazandaran dake arewacin Iran ne ya sanar da bankado da kuma rusa gungun masu yi wa abokan gabar leken asiri, ta hanyar amfani da ‘yan kasashen waje da masu zuwa yawon bude ido.
Kwamandan dakarun kare juyin juya halin na Mazandaran ya kara da cewa; Da dama daga cikin wadanda suke leken asirin suna fakewa ne a karkashin kamfanoni na kasuwanci, cibiyoyin al’adu da kuma kungiyoyin agaji.
Bugu da kari kwamandan na dakarun kare juyin juya halin musulunci a gundumar ta Mazandaran ya kuma ce, bayan sa ido na jami’an leken asiri, dakarun na IRGC, sun yi nasarar gano su, da kuma rusa shekarsu ta leken asiri.