Babban kwamandan dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran ya bayyana cikakken shirin Iran na tunkarar duk wani mataki na wuce gona da iri a daidai lokacin da ake ci gaba da fuskantar barazanar daukar matakin soji kan kasar.
Manjo Janar Hossein Salami ya bayyana hakan ne yau Alhamis, yayin da rahotanni ke nuni da cewa, Amurka ta sanya ofisoshin jakadancinta da sansanonin sojinta da ke yammacin Asiya cikin shirin ko-ta-kwana saboda fargabar yiwuwar kai wa Iran hari.
“A wasu lokuta makiya suna yi mana barazana da daukar matakin soji, mun sha bayyanawa, kuma muna maimaitawa a yau, cewa mun shirya tsaf don fuskantar duk wani yanayi,” in ji shi.
“Muna da kwarewa, mun karfafa karfinmu tare da samar da dabaru a cikin tsare-tsarenmu.
Muna sa ido sosai kan sojojin abokan gaba kuma mun aiwatar da shirye-shiryenmu.” Inji shi.
Har ila yau babban kwamandan dakarun kare juyin juya halin Musulunci ya gargadi makiya game da duk wani gigi, ya kuma shawarce su da su yi la’akari da illolin da ayyukansu zasu haifar.