Iraniyawa na bikin tunawa da karbe ofishin jakadancin Amurka a Tehran a 1979

A Iran dubban ‘yan kasar ne suka taru a Tehran da kuma birane sama da 900 a fadin kasar don tunawa da karbe ofishin jakadancin

A Iran dubban ‘yan kasar ne suka taru a Tehran da kuma birane sama da 900 a fadin kasar don tunawa da karbe ofishin jakadancin Amurka a 1979, bikin da ake wa lakabi da ‘’Ranar Yaki da Girman Kai ta Duniya’’ A kasar.

Dalibai, matasa, malamai, da iyalai ne suka halarci tarurrukan na yau Talata suna masu Allah wadai da ayyukan Amurka da Isra’ila, gami da harin da suka kai wa Iran a watan Yuni.

Mahalarta tarukan dauke da tutocin Iran da hotunan wadanda suka yi shahada a hare-haren Isra’ila da Amurka yayin da suke rera taken “Mutuwa ga Amurka” da “Mutuwa ga Isra’ila.”

Jami’ai daga cibiyoyin gwamnati da na soji, iyalan shahidai, da tsoffin sojoji yakin da Irak na shekarun 1980 a kan Iran suma sun halarci taron.

A Tehran, zanga-zangar ta fara a Dandalin Falasdinu kuma ta nufi tsohon Ofishin Jakadancin Amurka, inda aka gabatar da jawabai, da ke Allah wadai da Amurka da Isra’ila.

A matsayin wani bangare na zanga-zangar, an nuna makamai masu linzami da na’urorin tace uranium na Iran a kan hanyoyi.

Mahalarta tarukan sun kuma kona tutar Amurka da Isra’ila don nuna fushinsu a tsawon shekaru da dama na zalunci.

Ranar 13 ga watan Aban a kalandar Iraniyawa ta kunshi ababe guda uku da tunawa dasu : Ranar Dalibai data samo asali daga kisan daliban da ke zanga-zanga a shekarar 1978 da Ranar Kasa ta Yaki da Girman Kai (karbe Ofishin Jakadancin Amurka a shekarar 1979) da korar Imam Khomeini zuwa Turkiyya a shekarar 1964.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments