Iran Zata Hana Amurka Samar da Hanya A yankin Caucasus Ko Rasha Bata taimaka ba

Babban mai bawa jagoran juyin juya halin musulunci Imam Sayyid Aliyul Khaminae shawara, wato Ali Akbar Wilayati ya bayyana cewa Iran zata hana America samar

Babban mai bawa jagoran juyin juya halin musulunci Imam Sayyid Aliyul Khaminae shawara, wato Ali Akbar Wilayati ya bayyana cewa Iran zata hana America samar da hanya a yankin Caucasus, ko da kasar rasha ta taimaka ko bata taimaka ba.

A wata hira na musamman da kamfanin dillancin labaran Tasnim, Ali Akbara wailayati ya yi watsi da wani shiri wai shi zangezur wanda an tsara zai hana kasar Armenia da Nakhchivan.

Da aka tambaye shi da maganar cewa Armenia zata bawa Amurka yankin haya na tsawon shekaru 99 masu zuwa, Wilayati ya bayyana cewa warin zai zama makabartan sojojin Donal trump, wannan ba hanya ce wanda Amurka ta mallaka ba.

Ya ce gwamnatin kasar Iran ta sha bayyana cewa bata amince da shirin Zangezur a yankin Caucasusu don yankin yana daga cikin yankuna masu hatsari a duniya. Kuma zai haddasa matsalolin tsaro ga kasr Iran.

Saboda shirin zai rarraba kasashen yakin da kuma batar da kasar Armenia gaba dayanta.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments