Iran Zata Dauki Bakoncin Taro Dangane Da Kasar Afganistan Da Tsaron Yankin

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Esma’il Baqai ya bada sanarwan cewa Tehran zata dauki bakoncin wasu kasashen yankin don tattaunawa dangane da harkokin tsaro

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Esma’il Baqai ya bada sanarwan cewa Tehran zata dauki bakoncin wasu kasashen yankin don tattaunawa dangane da harkokin tsaro a kasashen yankin musamman tsakanin Afganisatan da Pakistan.

Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Baghae na fadar haka a safiyar yau Jumma’a ya kuma kara da cewa kafin haka kasashen Qatar, Turkiya da Saudiya sun yi kokarin sasanta kasashen Afganistan da Pakisatan dangane da rikice-rikicen da ke aukuwa tsakanin kasashen biyu a cikin yan watannin da suka gabata.

Ya ce gwamnatin kasar Iran tana son ganin an kawo karshen duk wata rigima tsakanin kasashen yankin saboda tana shafar al-amura da dama a yankin.

Labarin ya kara da cewa taron wanda za’a gudanar a a mako mai zuwa zai sami halattan wakilai daga kasashen Afghanistan Pakistan, Tajikistan, Uzbekistan, Turkmenistan, China da Russia.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted