Iran ta ce za ta fifita diflomatisyya ta tsakaninta da kasashe makobtanta na yankin.
Ministan harkokin wajen kasar ne Abbas Araghchi ya jaddada aniyar kasar kan harkokin diflomasiyya a yankin, yana mai bayyana cewa kasashen da ke makwabtaka da kasar na cikin tsarin Jamhuriyar Musulunci.
“Makwabtanmu sune fifikonmu,” in ji ministan harkokin wajen Iran a cikin wani sako da aka wallafa a shafinsa na X.
Mista Araghchi ya tattauna da takwarsana na Omani, Badr bin Hamad Al Busaidi, a Muscat, babban birnin kasar Omani, inda suka tattauna muhimman batutuwan da suka shafi kasashen biyu da na shiyya-shiyya.
Babban burinmu shi ne kare zaman lafiya da kwanciyar hankali ta hanyar diflomasiyya.
Ziyarar ta Araghchi a birnin Muscat na zuwa ne a daidai lokacin da rikicin yankin ke ci gaba da ruruwa, sakamakon kisan kiyashin da gwamnatin Isra’ila tare da goyon bayan Amurka ke aiwatarwa a zirin Gaza da kuma yadda ake ci gaba da kai munanan hare-hare a wasu wurare a yankin musamman a Syria da Lebanon.