Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya gargadi Amurka game da gabatar da “bukatun da ba su dace ba” a tattaunawar dake tsakanin kasashen biyu, yana mai cewa Jamhuriyar Musulunci ta Iran za ta ci gaba da inganta sinadarin Uranium tare da ko ba tare da wata yarjejeniya da Washington ba.
Abbas Araghchi na mayar da martani ne ga furucin da manzon shugaban kasar Amurka a yankin Steve Witkoff ya yi cewa, Washington ba za ta bar Iran ta samu karfin sarrafa sinadarin Uranium ba, ko da kashi 1%.
Mista Araghchi, wanda shi ne babban mai shiga tsakani na Iran, ya shaida wa manema labarai cewa, irin wadannan kalamai sun kauce wa tattaunawar.
Har ila yau ministan harkokin wajen na Iran ya kara da cewa Tehran a shirye take ta nuna cewa ba ta da niyyar kera makaman kare dangi idan Amurkawa suka so.
A wata hira da gidan talabijin na ABC na “Wannan Makon,” Witkoff ya ce “Jan layi” na gwamnatin Trump a tattaunawar nukiliya da Iran shi ne cewa Tehran ba ta da ikon inganta makamashin Uranium.
“Idan Amurka na son tabbatar da cewa Iran ba ta mallaki makaman nukiliya ba, yarjejeniya tana kan gaba, kuma a shirye muke mu shiga tattaunawa mai mahimmanci don cimma matsaya da za ta tabbatar da wannan sakamako a cikin dogon lokaci.
Har ila yau ministan harkokin wajen na Iran ya ce nan ba da jimawa ba za a gudanar da zagaye na gaba na tattaunawa tsakanin Iran da Amurka.