Iran Za Ta Aike Da Tawaga A Matakin Koli Don Halartar Jana’izar Nasrallah

Iran ta bayyana cewa za ta aike da tawaga a matakin koli zuwa jana’izar mirigayi babban sakataren kungiyar Hizbollah ta kasar Lebanon Hassan Nasrallah. Da

Iran ta bayyana cewa za ta aike da tawaga a matakin koli zuwa jana’izar mirigayi babban sakataren kungiyar Hizbollah ta kasar Lebanon Hassan Nasrallah.

Da yake sanar da hakan kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Esmaeil Baghaei ya ce kasar za ta halarci gagarumin bikin mai matukar muhimmanci,

Tunda farko dai kungiyar gwagwarmayar Hizbullah ta kasar Lebanon ta sanar da cewa tawagogin kasashe 79 za su halarci bikin tunawa da marigayi babban sakataren kungiyar Sayyid Hassan Nasrallah da kuma shugaban majalisar zartarwarta Sayyid Hashem Safieddine.

Sheikh Ali Daher, kodinetan babban komitin jana’izar Nasrallah da Safieddine, ya bayyana cewa bikin da aka shirya yi a ranar 23 ga watan Fabrairu, zai kasance “ranar tunawa da shugaban wanda aka zalunta a kan ma’abuta girman kai, da kuma shahidan bil’adama a kan mulkin mallaka”.

Ya kara da cewa jana’izar za ta ci gaba da zaburar da mutane masu ‘yanci a duniya shekaru da dama masu zuwa.”

Daher ya yi nuni da cewa bikin zai dauki kimanin sa’a daya kuma zai hada da jawabin babban sakataren kungiyar Sheikh Naim Qassem.

Sayyid Nasrallah ya yi shahada ne a yayin harin bam da Isra’ila ta kai a kudancin birnin Beirut a ranar 27 ga Satumba, 2024, Shi kuwa Safieddine ya yi shahada a lokacin harin da Isra’ila ta kai a watan Oktoban 2024.

Kungiyar Hizbullah ta dage bikin jana’izar shugabannin biyu saboda fargabar hare-haren Isra’ila a yayin bikin.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments