Trump Ya Yi Amai Ya Lashe Game Da Barazanar Kai Wa Tashoshin Wutar Lantarkin Iran Hari

Bayan da ya kasa gamsar da NATO da wasu kasashe domin bude mashigar Hormuz da karfi, Trump ya yi barazanar rusa dukkanin tashoshin wutar lantarki
Trump Ya Yi Amai Ya Lashe Game Da Barazanar Kai Wa Tashoshin Wutar Lantarkin Iran Hari

Bayan da ya kasa gamsar da NATO da wasu kasashe domin bude mashigar Hormuz da karfi, Trump ya yi barazanar rusa dukkanin tashoshin wutar lantarki da makamashi na Iran.
Nan take rundunar sojin Iran ta mayar da martani da cewa idan Amurka ta aiwatar da wannan barazana, to abubuwa kamar haka za su faru:
Za a rufe mashigar Hormuz baki daya har sai bayan kamala gyara tashoshin Iran da aka bata, Za su kai hari a kan dukkanin tashoshin wutar lantarki da makamashi na Iran.
Za su kai hari a kan dukkanin kamfanonin wutar lantarki na ASmurka ko kuma wadanda Amurkawa ked a hannun jaria cikinsu a yankin.
Zasu kai hari a kan tashoshin makamshi da na wutar lantarki a cikin dukkanin kasashen yankin gabas ta tsakiya da suke daukar bakuncin sansanonin sojin Amurka.
Daga karshe dai, Trump ya sanar da cewa ya dakatar da kai hari kan tashoshin wutar lantarki na Iran daga nan zuwa kwanaki biyar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted